lis din Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa
عربي Turanci urdu
‌Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa
عربي Turanci urdu
‌Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi
عربي Turanci urdu
‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki
عربي Turanci urdu
‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce
عربي Turanci urdu
An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba
عربي Turanci urdu
Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi
عربي Turanci urdu
‌Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta
عربي Turanci urdu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr
عربي Turanci urdu
‌Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu
عربي Turanci urdu
Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah?
عربي Turanci urdu
‌Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba
عربي Turanci urdu
Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina?
عربي Turanci urdu
Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi
عربي Turanci urdu
‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce
عربي Turanci urdu
Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci
عربي Turanci urdu
Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi
عربي Turanci urdu
Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?
عربي Turanci urdu
Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira
عربي Turanci urdu
Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi
عربي Turanci urdu
To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa
عربي Turanci urdu
Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su
عربي Turanci urdu
Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa
عربي Turanci urdu
Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta
عربي Turanci urdu
Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba
عربي Turanci urdu
Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu
عربي Turanci urdu
Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku
عربي Turanci urdu
Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka
عربي Turanci urdu
‌Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami
عربي Turanci urdu
‌Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya
عربي Turanci urdu
‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani
عربي Turanci urdu
‌Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya
عربي Turanci urdu
Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi
عربي Turanci urdu
Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira
عربي Turanci urdu
‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa
عربي Turanci urdu
‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana
عربي Turanci urdu
‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne
عربي Turanci urdu
‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da azabar ƙabari, ya Allah Ka baiwa raina tsoranta, Ka tsarkaketa, Kai ne mafificin Mai tsarkaketa, Kai ne majiɓincin lamarinta kuma shugabanta, Ya Allah ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani, da zuciyar da bata risina, da zuciyar da ba ta ƙoshi, da addu'ar da ba'a amsarta
عربي Turanci urdu
‌Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi
عربي Turanci urdu
‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma
عربي Turanci urdu
‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku
عربي Turanci urdu
‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa
عربي Turanci urdu
Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah
عربي Turanci urdu
‌Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima
عربي Turanci urdu
‌Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi
عربي Turanci urdu
‌Mai wuce wa ta gaban mai sallah da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alheri gareshi da ya wuce ta gabansa
عربي Turanci urdu
‌Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne
عربي Turanci urdu
‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya
عربي Turanci urdu
‌Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta
عربي Turanci urdu
‌Lallai waɗannan masallatan badan fitsari aka yi su ba, ko dan ƙazanta , kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka, da sallah da kuma karatun alƙur'ani
عربي Turanci urdu
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi
عربي Turanci urdu
‌Kada ɗayanku ya yi tsarki da ƙasa da duwatsu uku
عربي Turanci urdu
‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta
عربي Turanci urdu
Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa
عربي Turanci urdu
Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri)
عربي Turanci urdu
‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa
عربي Turanci urdu
‌Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai
عربي Turanci urdu
Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram
عربي Turanci urdu
An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka
عربي Turanci urdu
Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta
عربي Turanci urdu
Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka
عربي Turanci urdu
Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so
عربي Turanci urdu
Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya
عربي Turanci urdu
Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah
عربي Turanci urdu
Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa
عربي Turanci urdu
Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne
عربي Turanci urdu
Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa
عربي Turanci urdu