عن سهل بن سعد الساعدي رضي الله عنه قال: جاء رجل إلى النبي -صلى الله عليه وآله وسلم- فقال: يا رسول الله، دُلَّنِي على عمل إذا عملته أحبني الله وأحبني الناس؟ «فقال ازهد في الدنيا يحبك الله، وازهد فيما عند الناس يحبك الناس».
[صحيح] - [رواه ابن ماجه]
المزيــد ...

Daga Sahal Dan Sa'ad Al'sa'idi Allah ya yarda da shi ya ce: wani Mutum ya zo wajen Annabi sai ya ce ya Manzon Allah, Nunamun wani akiki idan nayi shi Allah zai so ni kuma Mutane Ma zasu so ni sai ya ce "Ka Guji Duniya Sai Allah ya so ka, ka guji abin hannun Mutane sai Mutane su so ka"
Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi

Bayani

Wani Mutum ya zo wajen Annabi yana neman ya shiryar da shi izuwa wani aiki da idan yayi shi zai zamanto masa sanadin samun soyayyar Allah da kuma soyayyar Mutane, sai Annabi ya shiryar da shi, izuwa wani aiki wanda ya tattare komai zai samar masa da soyayyar Allah da kuma soyayyar Mutane, sai Annabi ya ce: "Ka guji Duniya" ai kada ka nemi komai a cikinta sai abinda kake bukatarsa kuma duk abinda baka bukata ka rabu da shi, da kuma duk abinda ba zai maka amfani ba a lahira, kuma kayi tsansteni da duk abinda zai cutar da Addininka, kuma ka nisanci abin duniya da mutane suke ta rubibin nema, to kuma idan ya kasance akwai wani abu a tsakaninka da dayansu wani abu ko kuma wani ciniki to ka kasance kamar yadda Annabi ya fada: "Allah yaji kan wani Mutum Mai sauki idan ya siyar kuma mai sauki idan ya zo siya, haka mai sauki idan zai biya, kuma mai saukin kai idan zai nemi a biya shi"; don ka zamanto abin so a wajen Allah.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin