Karkasawa: Falaloli da Ladabai .

عن عائشة رضي الله عنها عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«إِنَّ أَبْغَضَ الرِّجَالِ إِلَى اللهِ الْأَلَدُّ الْخَصِمُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2457]
المزيــد ...

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce:
"Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 2457]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - yana ƙin mai tsananin husuma, kuma mai yawaitata daga cikin mutane, wanda ba ya karɓar jawuwa ga gaskiya, kuma yana ƙoƙarin tunkuɗeta da jayayyarsa, ko ya yi husuma da gaskiya, sai dai cewa yana kai matuƙa a cikin husuma, kuma yana fita daga iyakar daidaituwa, yana jayayya ba tare da ilimi ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Neman haƙƙin wanda aka zalunta da gaskiya ta hanyar kai ƙara, ba ya shiga cikin babin husumomi ababen zargi.
  2. Jayayya da husuma suna daga illolin harshe waɗanda suke sabbaba rabuwa da juya baya a tsakaknin musulmai.
  3. Jayayya abar yabo ce, idan ta kasance a kan gaskiya ne kuma usulubinta mai kyau, kuma tana kasancewa abar zargi idan ta kasance don dawo da gaskiya ne da tabbatar da ɓarna, ko ta kasance ba tare da hujja ba ko dalili.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)