عن جُبَير بن مُطْعِم رضي الله عنه أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول:
«لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعُ رَحِمٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2556]
المزيــد ...
Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa;
"Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2556]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yanke abin da yake wajaba daga 'yan uwansa na haƙƙoƙi, ko ya cutar da su ya munana musu, to, ya cancanci ba zai shiga aljanna ba.