عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال النبي صلى الله عليه وسلم:
«لَا تَسُبُّوا الْأَمْوَاتَ، فَإِنَّهُمْ قَدْ أَفْضَوْا إِلَى مَا قَدَّمُوا».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 1393]
المزيــد ...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1393]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haramcin zagin matattu da afkawa a cikin mutuncinsu, kuma wannan yana daga munanan ɗabi'u; domin sun kai zuwa abin da suka gabatar da shi na ayyuka na gari ko na banza, kamar yadda wannan zagin ba ya isa zuwa garesu, to, lallai cewa yana cutar da rayayyu.