+ -

عَن أَبِي بُرْدَةَ بْنِ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
وَجِعَ أَبُو مُوسَى وَجَعًا شَدِيدًا، فَغُشِيَ عَلَيْهِ وَرَأْسُهُ فِي حَجْرِ امْرَأَةٍ مِنْ أَهْلِهِ، فَلَمْ يَسْتَطِعْ أَنْ يَرُدَّ عَلَيْهَا شَيْئًا، فَلَمَّا أَفَاقَ، قَالَ: أَنَا بَرِيءٌ مِمَّنْ بَرِئَ مِنْهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَرِئَ مِنَ الصَّالِقَةِ وَالحَالِقَةِ وَالشَّاقَّةِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1296]
المزيــد ...

Daga Abu Burdah ɗan Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Abu Musa ya yi ciwo ciwo mai tsanani, sai ya suma alhali kansa yana cikin ɗakin wata mata daga iyalansa, bai samu damar da zai dawo mata da komai ba, lokacin da ya farka, ya ce: Ni na kuɓuta (na barranta) daga wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta da shi, Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga mai ɗaga murya da mai aske kanta da mai tsaga kayanta.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1296]

Bayani

Abu Burda - Allah Ya yarda da shi - ya hakaito cewa babansa Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya yi rashin lafiya, rashin lafiya mai tsanani har ya suma, kuma kansa ya zama a ɗakin wata mata daga cikin iyalansa, sai ta yi ihu ta yi masa kukan mutuwa, bai samu damar da zai mayar mata da komai ba saboda sumansa. Lokacin da ya farka ya ce: Lallai cewa shi ya kuɓuta (ya barranta) daga wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga gare shi, lallai cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - haƙiƙa ya kuɓuta daga: Al-Saliƙah: Ita ce mai ɗaga muryarta a lokacin musiba. AlHaliƙah: Ita ce wacce take aske gashin kanta a lokacin musiba. Asshaƙƙah: Ita ce wacce take tsaga tufafinta a lokacin musiba. Domin cewa su suna daga al'amuran Jahiliyya, kai an yi umarni da yin haƙuri a lokacin musiba, da neman ladanta ga Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga tsaga tufa, da aske gashi, da ɗaga murya a lokacin afkuwar musibu, kuma cewa hakan yana daga manyan zunubai.
  2. Baƙin ciki da kuka banda kururuwa da ɗaga murya ba haramun ba ne, hakan ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah, kawai shi tausayi ne.
  3. Haramcin fushi daga ƙaddarorin Allah masu sa raɗaɗi da faɗa ko aikatawa.
  4. Wajabcin haƙuri a lokacin afkuwar musibu.