Karkasawa: Aqida .
+ -

عن أبي ذر رضي الله عنه:
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيمَا رَوَى عَنِ اللهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى أَنَّهُ قَالَ: «يَا عِبَادِي إِنِّي حَرَّمْتُ الظُّلْمَ عَلَى نَفْسِي، وَجَعَلْتُهُ بَيْنَكُمْ مُحَرَّمًا، فَلَا تَظَالَمُوا، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ ضَالٌّ إِلَّا مَنْ هَدَيْتُهُ، فَاسْتَهْدُونِي أَهْدِكُمْ، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ جَائِعٌ إِلَّا مَنْ أَطْعَمْتُهُ، فَاسْتَطْعِمُونِي أُطْعِمْكُمْ، يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ عَارٍ إِلَّا مَنْ كَسَوْتُهُ، فَاسْتَكْسُونِي أَكْسُكُمْ، يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ تُخْطِئُونَ بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَأَنَا أَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا فَاسْتَغْفِرُونِي أَغْفِرْ لَكُمْ، يَا عِبَادِي إِنَّكُمْ لَنْ تَبْلُغُوا ضَرِّي فَتَضُرُّونِي، وَلَنْ تَبْلُغُوا نَفْعِي فَتَنْفَعُونِي، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ كَانُوا عَلَى أَتْقَى قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ مِنْكُمْ مَا زَادَ ذَلِكَ فِي مُلْكِي شَيْئًا، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ كَانُوا عَلَى أَفْجَرِ قَلْبِ رَجُلٍ وَاحِدٍ مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِنْ مُلْكِي شَيْئًا، يَا عِبَادِي لَوْ أَنَّ أَوَّلَكُمْ وَآخِرَكُمْ وَإِنْسَكُمْ وَجِنَّكُمْ قَامُوا فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ فَسَأَلُونِي فَأَعْطَيْتُ كُلَّ إِنْسَانٍ مَسْأَلَتَهُ مَا نَقَصَ ذَلِكَ مِمَّا عِنْدِي إِلَّا كَمَا يَنْقُصُ الْمِخْيَطُ إِذَا أُدْخِلَ الْبَحْرَ، يَا عِبَادِي إِنَّمَا هِيَ أَعْمَالُكُمْ أُحْصِيهَا لَكُمْ ثُمَّ أُوَفِّيكُمْ إِيَّاهَا، فَمَنْ وَجَدَ خَيْرًا فَلْيَحْمَدِ اللهَ، وَمَنْ وَجَدَ غَيْرَ ذَلِكَ فَلَا يَلُومَنَّ إِلَّا نَفْسَهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2577]
المزيــد ...

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci, ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku, ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku, ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku, ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku, Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni, ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi, Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka - Ya faɗi cewa: Ya haramta zalunci a kan kansa, kuma Ya sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin bayinsa, kada wani ya zalunci wani. Kuma cewa halitta gaba ɗayansu ɓatattu ne daga hanyar gaskiya sai da shiriyar Allah da dacewarsa, wanda ya roketa zai datar dashi kuma ya shiryeshi, kuma cewa halitta mabuƙata ne zuwa ga Allah masu buƙata ne gareshi a dukkanin buƙatunsu, wanda ya roƙi Allah zai biya buƙatarsa Ya kuma isar masa, kuma cewa suna yin zunubai dare da rana, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Yana suturtawa yana yafewa a yayin roƙon bawa gafara, kuma cewa su ba za su iya cutar da Allah ba, ko su amfanar da Shi da komai ba, kuma da ace sun kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya, to, takawarsu ba za ta ƙara komai a mulkin Allah ba, da sun kasance a kan mafi fajircin zuciyar mutum ɗaya, to, fajircinsu ba zai tauye komai daga mulkinsa ba; domin cewa su raunana ne mabuƙata a gurin Allah, masu buƙatuwa zuwa gareshi a kowane hali da zamani da wuri, Shi ne Mawadaci - tsarki ya tabbatar masa -. kuma cewa da ace sun tsaya a bigire ɗaya mutanensu da aljanunsu, na farkonsu da na ƙarshensu suna roƙon Allah sai Ya ba wa kowane ɗaya daga cikinsu abin da ya roƙa, hakan ba zai tauye komai daga abinda ke wurin Allah ba, kamar allura ce da ake shigar da ita kogi sannan a fitar da ita, to, kogin ba zai ragu da komai ba, wannan don cikar wadatarsa tsarki ya tabbatar masa.
Kuma Allah - tsarki ya tabbatar masa Yana kiyaye ayyuakan bayi, Yana tsaresu musu su, sannan Ya cika musu su a ranar al-ƙiyama, wanda ya samu sakamakon aikinsa alheri, to, ya godewa Allah a bisa dacewa da ya yi ga biyayya gareshi, wanda ya samu sakamakon aikinsa wani abu saɓanin hakan, to, kada ya zargi kowa sai zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna wacce ta ja shi zuwa taɓewa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الليتوانية الدرية الصربية الطاجيكية الكينياروندا الرومانية المجرية التشيكية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudusi ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu kususiyyar Al-ƙur'ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, na bauta da karantashi, da tsarki saboda shi da tahaddi (fito na fito) da gajiyarwa da wanin hakan.
  2. Abin da yake faruwa ga bayi na ilimi ko shiriya, to, da shiriyar Allah ne da kuma koyarwarsa.
  3. Abin da yake samun bawa na alheri, to, daga falalar Allah ne - Maɗaukakin sarki -, abin da kuma ya sameshi na sharri, to, daga kansa ne da kuma son ransa.
  4. Wanda ya kayautata, to, da dacewar Allah ne, kuma sakamakonsa falala ce daga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya munana, to, kada ya zargi kowa sai kansa.