عن الْأَغَرِّ رضي الله عنه، وَكَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يَا أَيُّهَا النَّاسُ تُوبُوا إِلَى اللهِ، فَإِنِّي أَتُوبُ فِي الْيَوْمِ إِلَيْهِ مِائَةَ مَرَّةٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2702]
المزيــد ...
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2702]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.