kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

:
عربي Turanci urdu
: .
عربي Turanci urdu
: .
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: @"Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
عربي Turanci urdu
"Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku* kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce wani dutse ana ce masa Jumdan, sai ya ce: "Ku tafi ! wannan Jumdan ne,@Masu kaɗaitawa sun rigaya*" Suka ce: Suwaye musu kaɗaitawa ya manzon Allah? ya ce: "Masu ambatan Allah da yawa maza da mata masu ambatan Allah".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara".
عربي Turanci urdu
"Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah".
عربي Turanci urdu
Shin ba zan gaya muku abin da nake son fada wa Allah ba? Mafi soyuwa ga magana ga Allah: Tsarki ya tabbata ga Allah da yabo
عربي Turanci urdu
A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da tashe: "Da wanda raina yake a hannunsa, da ba ku yi zunubi ba, da Allah zai fita daga gare ku, kuma ya zo da mutanen da suka yi zunubi, kuma suna neman gafara daga Allah Madaukaki, kuma zai gafarta musu."
عربي Turanci urdu
"Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"
عربي Turanci urdu
Allah baiyi izini ga Annabi da wani Abu ba kamar yadda yayi izini da ya kawata Muryasa da Qur'ani
عربي Turanci urdu
"Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati*, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".
عربي Turanci urdu
Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "@Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku*", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci Sinhalese
Sauran mutanen kirki babu abin bauta sai Allah kuma tsarki ya tabbata ga Allah, Allah ya fi girma kuma godiya ta tabbata ga Allah kuma babu wani karfi a kusa kuma babu wani karfi sai Allah
عربي Turanci urdu
Dan Adam bai taba aikata wani aiki ba wanda ai tserar da shi daga Azabar Allah Kamar Ambaton Allah
عربي Turanci urdu
Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: @"Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne"*, Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".
عربي Turanci urdu
"Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
عربي Turanci urdu