عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَقِيتُ إِبْرَاهِيمَ لَيْلَةَ أُسْرِيَ بِي فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، أَقْرِئْ أُمَّتَكَ مِنِّي السَّلاَمَ، وَأَخْبِرْهُمْ أَنَّ الجَنَّةَ طَيِّبَةُ التُّرْبَةِ عَذْبَةُ الْمَاءِ، وَأَنَّهَا قِيعَانٌ، وَأَنَّ غِرَاسَهَا سُبْحَانَ اللهِ وَالحَمْدُ لِلَّهِ وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرُ».
[حسن بشواهده] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3462]
المزيــد ...
Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce, kuma ita faƙo ce kuma dashenta (shi ne): Subhanallah, (tsarki ya tabbata ga Allah), Alhamdulillah (godiya ta tabbata ga Allah), Lailaha Illallahu, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)".
- [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3462]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.