عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ سمعتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقولُ:
«أَلاَ إِنَّ الدُّنْيَا مَلْعُونَةٌ، مَلْعُونٌ مَا فِيهَا، إِلاَّ ذِكْرُ اللهِ وَمَا وَالاَهُ وَعَالِمٌ أَوْ مُتَعَلِّمٌ».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 2322]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 2322]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duniya da abinda ke cikinta abin ƙine a wurin Allah abin zargi abin bari abin nisantarwa, kuma abinda ke cikinta abin bari ne ba abin yabo bane; dan kasancewarta da dukkan abinda ke cikinta yana shagaltarwa daga barin Allah, kuma yana nisantarwa daga gare shi, saidai ambatan Allah da abinda ya kusance shi ya zama yana da jinsi da shi, cikin abinda Allah Ya so shi, ko masanin ilimi na shari'a wanda yake koyar da mutane, ko mai neman ilimin shari'a ɗin.