عَنِ الزُّبَيْرِ بْنِ العَوَّامِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَأَنْ يَأْخُذَ أَحَدُكُمْ حَبْلَهُ، فَيَأْتِيَ بِحُزْمَةِ الحَطَبِ عَلَى ظَهْرِهِ، فَيَبِيعَهَا، فَيَكُفَّ اللَّهُ بِهَا وَجْهَهُ خَيْرٌ لَهُ مِنْ أَنْ يَسْأَلَ النَّاسَ أَعْطَوْهُ أَوْ مَنَعُوهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 1471]
المزيــد ...
Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1471]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin mutane ya yi aiki kowane irin aiki ne koda zai ɗauki igiya ne, ya tattara itatuwa a gadan bayansa sai ya saida shi ya ci daga gare shi, ko ya yi sadaka da shi ya wadata daga mutane da shi kuma ya kare fuskarsa daga ƙasƙancin roƙo; shi ne ya fiye masa alheri daga ya tambayi mutane su ba shi ko su hanashi, roƙon mutane ƙasƙanci ne, mumini kuwa maɗaukaki ne ba ƙasƙantacce ba ne.