عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ وَفَاتِهِ بِثَلَاثٍ يَقُولُ:
«لَا يَمُوتَنَّ أَحَدُكُمْ إِلَّا وَهُوَ يُحْسِنُ بِاللهِ الظَّنَّ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2877]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin wafatinsa da (kwana) uku yana cewa:
"Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2877]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da musulmi cewa kar ya mutu sai shi yana kyautatawa Allah zato da rinjayarwarsa ɓangaren ƙauna a lokacin mutuwa da cewa Allah Zai yi masa rahama kuma Zai yi masa rangwame, domin cewa tsoro abin nema ne dan kyautata aiki, wancan halin ba halin ayyuka ba ne, abin nema a cikinsu (shi ne) rinjayar ƙauna.