kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: @Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa*".
عربي Turanci urdu
"Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta*", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
عربي Turanci urdu
"Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
عربي Turanci urdu
"Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyya, kaɗai mutum (ana bashi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "@Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne*".
عربي Turanci urdu
Imanin ɗayanku ba ya cika har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama da babansa da ‘ya’yansa da mutane bakiɗaya.
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa".
عربي Turanci urdu
"Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki".
عربي Turanci urdu
Idanun da wuta bata taba su ba: ido mai kuka saboda tsoron Allah, ido mai kiyaye hanyar Allah.
عربي Turanci urdu
"Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".
عربي Turanci urdu
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: @"Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya ji tsoronsa ya fi yawa a ciki, kuma duk wanda ya kai matakin kasa, to ya sami matsayi, kawai dai kayan Allah suna da daraja, in ba haka ba kayan Allah ne Aljanna.
عربي Turanci urdu
"Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne,* ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".
عربي Turanci urdu
"Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya*, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi. Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
عربي Turanci urdu
Ni manzon Allah ne zuwa gare ku, cewa Allah ya ƙaunace ku kamar yadda kuka ƙaunace shi a cikinsa
عربي Turanci urdu
A cikin Madina akwai mazaje da ba ku taka ba, kuma ba ku haye kwari ba, sai dai idan suna tare da ku wadanda aka daure da cuta
عربي Turanci urdu
Lallai Allah Madaukakin Sarki yayi mun wahayi cewa ku Kaskantar da kanku, ha yadda babu wani da zai yi alunci kan wani, kuma kada daya ya yi fariya akan wani
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci Indonisiyanci
Amma bayan haka, na rantse da Allah na ba mutumin kuma ina yin addu'a ga mutumin, kuma wanda nake kira mafi soyuwa a gare ni fiye da wanda aka ba shi
عربي Turanci urdu
Mutane Kamar Ma'adanan Zinare da Azurfa ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kuma Rayuka Kamar Rundunar yaki ce, duk wanda suka San juna sai su Saba, wanda kuma suka saba kuma sai suki jituwa
عربي Turanci urdu