عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ عَدْوَى وَلاَ طِيَرَةَ، وَلاَ هَامَةَ وَلاَ صَفَرَ، وَفِرَّ مِنَ المَجْذُومِ كَمَا تَفِرُّ مِنَ الأَسَدِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5707]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5707]
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin al'amuran Jahiliyya (maguzawa) dan gargaɗi daga gare su, da kuma bayanin al'amari yana hannun Allah, kuma wani abu ba ya kasancewa sai da umarninSa da ƙaddarawarSa, su ne:
Na farko: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna zatan cewa cuta tana yaɗuwa da kanta; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga ƙudirce tashin cuta daga mara lafiya zuwa ga mai lafiya da ɗabi'arta; Allah Shi ne Mai tasarrufi a cikin kasantattu; kuma Shi ne wanda Yake saukar da cuta kuma Yake ɗauketa, hakan ba ya faruwa saida nufinSa da ƙaddarawarSa.
Na biyu: Mutanen Jahiliyya sun kasance idan sun fita dan wata tafiya ko kasuwanci, sai su yi wa tsuntsu tsawa, idan ya tashi ɓangaren dama sai su yi murna, idan ya tashi ɓangaren hagu sai su canfa su dawo, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga wannan canfin da tsuntsu, ya kuma bayyana cewa hakan akida ce ɓatacciya.
Na uku: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna cewa: Idan mujiya ta faɗo a kan wani gida sai musiba ta samu mutanen wannan gidan; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani game da canfa hakan.
Na huɗu: Ya yi hani daga canfa watan Safar, shi ne wata na biyu daga watannin ƙamariyya. (Wasu kuma) suka ce Safar shi ne: Wata micijiya ce da take a ciki tana samun dabbobi da mutane, suna riya cewa ita ce mafi tsananin yaɗuwa daga cutar kirci; sai ya kore wannan akidar.
Na biyar: Ya yi umarni da nisantar wanda aka shafa da cutar kuturta kamar yadda zaka nisanci zaki, hakan dan bai wa kai kariya da kuma nema masa kuɓuta da kuma aikata sabubban da Allah ya yi umarni da su. Kuturta: Wata cuta ce da gaɓɓan mutum suke cin juna daga gareta.