عَن عُمَرَ بنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«لَا تُطْرُونِي كَمَا أَطْرَتِ النَّصَارَى ابْنَ مَرْيَمَ؛ فَإِنَّمَا أَنَا عَبْدُهُ، فَقُولُوا: عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 3445]
المزيــد ...

Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari ne ya rawaito shi] - [Sahih Al-Bukhari - 3445]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gargadarwa daga ketare iyakar shari'a a girmamawa da yabo; domin cewa hakan yana kaiwa zuwa ga shirka.
  2. Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi akan sa ya afku a cikin wannan al'ummar, sai wasu mutane suka wuce gona da iri a Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wasu mutanen kuma a iyalan gidansa, wasu mutanen kuma a waliyyai, sai suka fada a cikin shirka.
  3. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi bawan Allah ne; dan ya bayyana cewa shi bawa ne wanda yake bauta ga Allah, ba ya halatta a juyar masa da wani abu daga abinda Ubangiji Ya kebanta da shi.
  4. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi Manzon Allah ne abin aikowa daga wurin Allah to gasgata shi da binsa ya wajaba.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)