+ -

عن عبد الله بن مسعود قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«هَلَكَ الْمُتَنَطِّعُون» قالها ثلاثًا.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2670]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Masu tsanantawa sun halaka" ya fadi hakan ne har sau uku.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2670]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da tabewar masu tsanantawa - ba tare da shiriya da ilimi ba - a addinin su da duniyar su, da kuma maganganun su da ayyuakan su, masu ketare iyakar shari'a da su wanda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأكانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin tsanantawa da dorawa kai abinda ba zai iyaba a cikin al'amura gaba dayan su, da kwadaitarwa akan nisantarhakan a kowane abu; musammanma a cikin ibadu da girmama salihai.
  2. Neman mafi cika a cikin ibadu da wasunsu al'amari ne abin yabo; kuma yana kasancewane ta hanyar bin shari'a.
  3. Son karfafa al'amari mai muhimmanci; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya maimaita wannan jumlar har sau uku.
  4. Martabar musulunci da kuma saukinsa.
Kari