عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال:
قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم كَلِمَةً وَقُلْتُ أُخْرَى، قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: «مَنْ مَاتَ وَهُوَ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللهِ نِدًّا دَخَلَ النَّارَ» وَقُلْتُ أَنَا: مَنْ مَاتَ وَهُوَ لَا يَدْعُو لِلهِ نِدًّا دَخَلَ الْجَنَّةَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4497]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4497]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya karkatar da wani abu daga abinda yake wajaba ya zama na Allah ne zuwa waninSa, kamar rokon wanin Allah - Madaukakin sarki - ko neman agaji ga waninSa, ya kuma mutu akan hakan to cewa shi yana daga 'yan wuta. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya kara cewa wanda ya mutu alhali ba ya hada wani abu da Allah to makomarsa tana aljanna.