عن عائشة أم المؤمنين وعبد الله بن عباس رضي الله عنهما قالا:
لَمَّا نَزَلَ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَفِقَ يَطْرَحُ خَمِيصَةً لَهُ عَلَى وَجْهِهِ، فَإِذَا اغْتَمَّ بِهَا كَشَفَهَا عَنْ وَجْهِهِ، فَقَالَ وَهُوَ كَذَلِكَ: «لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى اليَهُودِ وَالنَّصَارَى، اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ» يُحَذِّرُ مَا صَنَعُوا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 435]
المزيــد ...
Daga Nana A'isha da Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - sun ce:
Lakacin da (wafati) ya saukar wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara yana rufe fuskarsa da wani mayafinsa, idan ya ji ya yi masa tsanani sai ya yaye shi daga fuskarsa, sai ya ce yana hakan: "Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai" yana gargaɗi game da abin da suka aikata.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 435]
Nana A'isha da Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - suna ba mu labarin cewa lokacin da wafati ya halartowa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara sanya wani yanki na riga a kan fuskarsa, idan numfashi ya wuyata a gareshi saboda magagin mutuwa, sai ya gusar da shi daga fuskarsa, sai ya faɗa a wannan halin mai tsanani: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, ya koresu daga rahamarSa; domin su sun gina masallatai a kan kaburburan Annabawansu, da ba don haɗarin al'amarin ba da bai ambace shi a irin wannan lokacin ba, saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana al'ummarsa da kamanceceniya da wannan aikin; domin yana daga aikin Yahudawa da Nasara, kuma hanya ce da za ta kai zuwa ga shirka da Allah - mai girma da ɗaukaka.