عن عبادة بن الصامت رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم "مَنْ شهِد أنْ لا إله إلا الله وحده لا شرِيك له وأنَّ محمَّدا عبده ورسُولُه، وأنَّ عِيسى عبدُ الله ورسُولُه وكَلِمَتُه أَلقَاها إِلى مريم ورُوُحٌ مِنه، والجنَّة حَقٌّ والنَّار حقٌّ، أَدْخَلَه الله الجنَّة على ما كان مِنَ العمَل".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abbadah Dan Samit daga Annabi: "Duk wanda ya shaida cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kadai wanda bashi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne kuma kalmarsa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare shi, kuma Aljanna Gaskiya ce haka wuta ma, to Allah zai shigar da shi Aljanna akan kowane irin aiki ya Mutu."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Wannan Hadisin yana bamu labarin cewa duk wanda ya furta Kalmar Tauhidi kuma yasan Ma'anarta kuma yayi aiki da abinda take koyarwa, kuma ya shaida da cewa Annabi Muhammad bawan Allah ne kuma Manzonsa ne, kuma yayi Ikirari da cewa Annabi Isa bawan Allah ne kuma Manzonsa nekuma cewa an halicce shi ne an halicce shi ne da kalmar kasance daga Nana Maryam sai ya kasance kuma Allah ya kubutar da Mahaifiyarsa daga abinda Yahudawa suka danganta mata, kuma yai Imani da samuwar Aljanna ga Muminai da kuma tabbatar wuta ga kafirai, kuma ya Mutu akan hakan to zai shiga Aljanna akan kuwa ko wane aiki yake yi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci
Manufofin Fassarorin