عن أبي موسى رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِنَّ اللهَ لَيُمْلِي لِلظَّالِمِ، حَتَّى إِذَا أَخَذَهُ لَمْ يُفْلِتْهُ» قَالَ: ثُمَّ قَرَأَ: «{وَكَذَلِكَ أَخْذُ رَبِّكَ إِذَا أَخَذَ الْقُرَى وَهِيَ ظَالِمَةٌ إِنَّ أَخْذَهُ أَلِيمٌ شَدِيدٌ}[هود: 102]»
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4686]
المزيــد ...
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4686]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu, to, lalle Allah maɗaukaki Yana saurarawa azzalumi ya jinkirta masa, ya tsawaita masa a rayuwarsa da dukiyarsa ba zai gaggauta masa uƙuba ba, to, idan bai tuba ba sai ya damƙe shi, kuma ba zai sake shi ba, ba kuma zai ƙyale shi ba sabo da yawan zaluncinsa.
Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karanta: Kuma haka damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu suna azzalumai, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce kuma mai tsanani ce.