kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".
عربي Turanci urdu
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "@Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya".
عربي Turanci urdu
"Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
عربي Turanci urdu
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "@Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci*, ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku, ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku, ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku, ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku, Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni, ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi, Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
عربي Turanci urdu
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba*)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
عربي Turanci urdu
"Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".
عربي Turanci urdu
Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura* yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??
عربي Turanci urdu
Meye banbancin wadannan?zuciyarsu na yin taushi in suka ji ayoyi bayyanannu,su kuma rikice in suka ji ayoyi masu rikitarwa".
عربي Turanci urdu
. : :
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: @ Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona*, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
عربي Turanci urdu
"Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
عربي Turanci urdu
"Yaku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi*, sai Ya ce: {Yaku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. [al-Mu'uminun: 51] . Kuma Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku} [al:Baƙara: 172] sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
عربي Turanci urdu
Lokacin da Allah ya halicci halitta, ya rubuta a cikin wani littafi, kuma yana tare da shi a kan karaga: Rahamata ta rinjayi fushina
عربي Turanci urdu
Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:@Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa*, Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa*, Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".
عربي Turanci urdu
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Madaukakin sarki ya ce: ‘@Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba*. Amma karyatawar shi gare Ni shi ne fadinsa: (Allah) ba zai dawo dani ba (bayan mutuwa) kamar yadda Ya halicce ni a farko, ba wai halittar ta farkon ita ce mafi sauki gareNi daga dawowa da shi ba, amma aibantaNi shi ne fadinsa a kaina: Allah Yana da Da, alhali Ni Daya ne kwal wanda ake nufinSa da bukata Ban haifa ba, ba’a kuma haifeNi ba, kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Ni".
عربي Turanci urdu
"Kursiyyu shi Bugirem kafafuwan, Kuma Al-Arshi ba'a iya Kaddara shi da komai
عربي Turanci urdu
Lallai cewa wani Bayahude ya zo wajen Annabi sai ya ce da shi ya muhammad, Cewa Allah ya rike Sammai kan Yatsa daya, Kuma Kassai Kan Yatsa daya, kuma Duwatsu kan Yatsa daya, kuma Bushiyu Kan Yatsa daya, Kuma Halittu kan Yatsa daya, sannan ya ce: Ni ne Sarki
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: @Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba*, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"
عربي Turanci urdu
‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu*, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".
عربي Turanci urdu
Ubangijinmu zai yaye Maqyagyamarsa, sai kowane Mumini yayi sujada a gare shi Mace da Namiji, sai Waxanda suka kasance suna Sujada a Duniya saboda riya da jiyarwa su tsaya, sai su tafi suyi Sujada sai bayansu ya Sandare baki xaya
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Kuma mamamkin Kishin Sa'ad ko ? o na rantse da Allah, Allah shi ne mafi kishi dagani, saboda kishin Allah ne ya haramta Alfasha, bayyananniya da Voyayyiya, kuma babu Mutumin da yafi Allah kishi
عربي Turanci urdu
Babu wani Mutum, ko kuma babu wani abu Mafi haquri kan cutarwar da Allah yaji daga gare su, lallai su suna cewa yana da Xa, Kuma lallai cewa shi yana basu lafiya kuma yana Azurta su
عربي Turanci urdu
Jahannama bata gushe ba tana cewa: Shin akawai wani Qari har sai Allah Mai xaukaka ya sanya Qafarsa a ciki, sai ta ce: ya ishe ni ya isheni, kuma ya rawaito wani vangaren zuwa wani
عربي Turanci urdu
: : : :
عربي Turanci urdu
Shin kuna cutar ganin rana da tsakar rana, ba cikin gajimare ba? Suka ce: A'a. Ya ce: Shin kuna shan wahala wurin ganin wata a daren cikakken wata, ba cikin gajimare ba?
عربي Turanci urdu
Allah yana Sunaye Chasa'in da Tara Xari babu xaya babu wanda zai Haddace su face ya shiga Al-janna, kuma shi xaya ne kuma yana son kaxaitawa
عربي Turanci urdu
Idan dayanku ya tsaya a cikin sallarsa, to yana rokon Ubangijinsa ne, ko kuma idan Ubangijinsa yana tsakaninsa da alqibla, don haka kada ku tofa wa ɗayanku rigarsa da sumba, amma a hagu ko ƙasan ƙafafunsa.
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira*. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: "@ Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?*"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.
عربي Turanci urdu
Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsa
عربي Turanci urdu
Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan Yatsa,sannan yace:Nine Mamallaki.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan.Sannan ya karanta:"Kuma basu kaddara Allah Hakikanin ikonsa ba, kuma Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama"?.Acikin wata Ruwaya ta Muslim:"Da Duwatsu da Bishiyu akan Yatsa,sannan ya girgizasu sannan yace:Nine Mamallaki,nine Allah".Kuma acikin wata Ruwaya ta Buhari:"Zai sanya Sammai akan Yatsa,kuma Ruwa da Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halitta akan Yatsa"
عربي Turanci urdu
"Allah Mai xaukaki zai naxe sammai da a ranar Al-qiyama sannan ya xaukesu da Hannunsa na Dama sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci? kuma sannan sai naxe qasa ma da Hannunsa na Hagu sannan ya ce: Ni ne Mai Mulki ina masu jabberanci?"
عربي Turanci urdu
Yana cewa :’ku yi ceto za ku sami sakamako Allah Ya na hukunci ne akan harshen Manzonsa da abinda Ya so’’
عربي Turanci urdu
Idan Allah Madaukakin Sarki yana son rahamar al'ummar da Annabin ta ya mallake ta a gaban ta, to ya sanya ta zama wuce gona da iri a hannun ta.
عربي Turanci urdu
Ni ne mafi cancantar abin da kuka yi wa bawa na.
عربي Turanci urdu
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa.
عربي Turanci urdu
Allah Madaukakin Sarki zai yi dariya ga wasu maza biyu da suka kashe juna suka shiga Aljanna. Wannan yana fada ne saboda Allah kuma ana kashe shi, sannan Allah ya tuba da wanda ya kashe shi, kuma ya mika wuya kuma ya yi shahada
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Idan Allah ya so yiwa wasu Mutane Azaba, sai Azabar ta sami wadanda suke cikin su, Sannan sai a tashe su a kan Ayyukansu"
عربي Turanci urdu
Yayin da Allah ya suranta Annabi Adam a cikin Al-janna ya barshi lokacin da Allah ya so ya barshi, sai ya sanya Iblis yana kewaya shi, yana kallonsa, yayin da ya ganshi yana ciki sai ya san cewa shi ba zai iya Mallakar kansa ba"
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
Idan Bawa ya Kusance ni da dani daya, sai nima na kusanceshi da tsawon Hannu, idan kuma ya kusance ni da tsawon danin Hannuwa biyu, kuma idan yazo mun yana mai tahowa sai in zo masa ina mai Sassarfa
عربي Turanci urdu
Lallai Allah shi mai Mai xaga farashi kuma mai saukar da shi Mai Yalwata Arziqi, kuma ni ina fatan in gamu da Allah babu wani xaya daga cikin ku da yake bina bashin Jini ko kuma Kuxi
عربي Turanci urdu
Lallai Allah Maxaukaki Mai Kunya ne kuma mai Sututwa, yana son Kunya da Suturtawa, saboda haka idan xayanku zai yi Wanka to ya suturta
عربي Turanci urdu
Lallai Allah ya ce: Idan Bawana ya fuskance ni da Xani xaya, to zan kusance shi da Zira'i, kuma idan ya Kusance ni da Zira'i to zan kusance shi faxin Hannaye, Kuma idan ya kusance da Xanin hannye biyu zan zo masa da Mafi gaggawa
عربي Turanci urdu
Haqiqa Khaulatu ta zo wajen Manzon Allah SAW yana kai qarar Mijin ta, kuma zancenta ya kasance yana Voyemun
عربي Turanci urdu
Lallai Allah yana halitattar kowane Mutum da aikin sa
عربي Turanci urdu
Allah shi ne Mai warkarwa, amma kai Mutum ne da yake tausasawa, Mai warkar da ita shi ne Mahaliccinta
عربي Turanci urdu
Wuta da Aljanna sunyi Jayayya, sai wuta ta ce: an zaveni saboda masu girman kai, da Masu jiji da Kai, kuma Aljanna ta ce: Ni kuma babu mai shiga ta sai raunanan Mutane da waxanda ba komai ba, da wacanda idonsu bai buxe da Duniya ba
عربي Turanci urdu
Za'a tashi Mutane Ranar Al-qiyama -ko kuma ya ce Bayi= tsirara basu da Kaciya
عربي Turanci urdu
Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana: «‌Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:@«‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».
عربي Turanci urdu
Ganin cewa kare na zaune a cikin kududdufi, kuma kusan kishirwa ta kashe shi, lokacin da wata karuwa ta ganta a matsayin karuwa ga Banu Isra'ila, don haka ta firgita da shi.
عربي Turanci urdu
Imani bayamane ne kuma Hikima ma bayamaniya ce
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Allah ya rubuta kyautaye akan kowane abu, to idan zakuyi kisa to ku kyautata kisan kuma idan zakuyi yanaka to ku kyautata yankan kuma dayaku ya wasa wukar tasa, kuma don ya hutar da abin yankansa
عربي Turanci urdu
"Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"
عربي Turanci urdu
Ka sani kai Abu Mas'ud cewa lallai Allah shi ne mafi iko akan ka akan wannan Yaron, sai na ce: ba zan qara dukan Bawa ba har abadan
عربي Turanci urdu
Ya Ubangiji ka taimake ni kada ka bada Nasara akaina, ka taimakeni kuma kada ka bada taimako akaina, kayi mun shiri kuma kada kayi mun Makirci a kaina, Kuma ka shiryar da ni kuma ka sauqaqe mun shiriya, kuma ka taimakeni kan wanda ya zalunce ni
عربي Turanci urdu