عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
قَدِمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَبْيٌ، فَإِذَا امْرَأَةٌ مِنَ السَّبْيِ قَدْ تَحْلُبُ ثَدْيَهَا تَسْقِي، إِذَا وَجَدَتْ صَبِيًّا فِي السَّبْيِ أَخَذَتْهُ، فَأَلْصَقَتْهُ بِبَطْنِهَا وَأَرْضَعَتْهُ، فَقَالَ لَنَا النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَتُرَوْنَ هَذِهِ طَارِحَةً وَلَدَهَا فِي النَّارِ؟» قُلْنَا: لاَ، وَهِيَ تَقْدِرُ عَلَى أَلَّا تَطْرَحَهُ، فَقَالَ: «لَلَّهُ أَرْحَمُ بِعِبَادِهِ مِنْ هَذِهِ بِوَلَدِهَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5999]
المزيــد ...
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -:
Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana:
«Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:«Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5999]
An zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wasu ribatattu daga (ƙabilar) Hawazin, sai ga shi a cikinsu akwai wata mace tana neman ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaron da ta ɗauke shi sai ta shayar da shi saboda cutuwa da tayi ta hanyar taruwar nono a cikin hantsarta, sai ta samu ɗanta a cikin ribatattu sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa sahabbansa: Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta? Muka ce: Ba zata jefa shi da yardarta ba har abada. Sai ya ce: Allah Ya fi jin tausayin bayinSa daga wannan matar da ɗanta.