+ -

عَن أبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ:
كُنَّا قُعُودًا حَوْلَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، مَعَنَا أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ فِي نَفَرٍ، فَقَامَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ بَيْنِ أَظْهُرِنَا، فَأَبْطَأَ عَلَيْنَا، وَخَشِينَا أَنْ يُقْتَطَعَ دُونَنَا، وَفَزِعْنَا، فَقُمْنَا، فَكُنْتُ أَوَّلَ مَنْ فَزِعَ، فَخَرَجْتُ أَبْتَغِي رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَتَّى أَتَيْتُ حَائِطًا لِلْأَنْصَارِ لِبَنِي النَّجَّارِ، فَدُرْتُ بِهِ هَلْ أَجِدُ لَهُ بَابًا؟ فَلَمْ أَجِدْ، فَإِذَا رَبِيعٌ يَدْخُلُ فِي جَوْفِ حَائِطٍ مِنْ بِئْرٍ خَارِجَةٍ - وَالرَّبِيعُ الْجَدْوَلُ - فَاحْتَفَزْتُ، فَدَخَلْتُ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَبُو هُرَيْرَةَ» فَقُلْتُ: نَعَمْ يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «مَا شَأْنُكَ؟» قُلْتُ: كُنْتَ بَيْنَ أَظْهُرِنَا، فَقُمْتَ فَأَبْطَأْتَ عَلَيْنَا، فَخَشِينَا أَنْ تُقْتَطَعَ دُونَنَا، فَفَزِعْنَا، فَكُنْتُ أَوَّلَ مَنْ فَزِعَ، فَأَتَيْتُ هَذَا الْحَائِطَ، فَاحْتَفَزْتُ كَمَا يَحْتَفِزُ الثَّعْلَبُ، وَهَؤُلَاءِ النَّاسُ وَرَائِي، فَقَالَ: «يَا أَبَا هُرَيْرَةَ» وَأَعْطَانِي نَعْلَيْهِ، قَالَ: «اذْهَبْ بِنَعْلَيَّ هَاتَيْنِ، فَمَنْ لَقِيتَ مِنْ وَرَاءِ هَذَا الْحَائِطَ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُسْتَيْقِنًا بِهَا قَلْبُهُ، فَبَشِّرْهُ بِالْجَنَّةِ»، فَكَانَ أَوَّلَ مَنْ لَقِيتُ عُمَرُ، فَقَالَ: مَا هَاتَانِ النَّعْلَانِ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ؟ فَقُلْتُ: هَاتَانِ نَعْلَا رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، بَعَثَنِي بِهِمَا مَنْ لَقِيتُ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُسْتَيْقِنًا بِهَا قَلْبُهُ، بَشَّرْتُهُ بِالْجَنَّةِ، فَضَرَبَ عُمَرُ بِيَدِهِ بَيْنَ ثَدْيَيَّ فَخَرَرْتُ لِاسْتِي، فَقَالَ: ارْجِعْ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ، فَرَجَعْتُ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَجْهَشْتُ بُكَاءً، وَرَكِبَنِي عُمَرُ، فَإِذَا هُوَ عَلَى أَثَرِي، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا لَكَ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ؟» قُلْتُ: لَقِيتُ عُمَرَ، فَأَخْبَرْتُهُ بِالَّذِي بَعَثْتَنِي بِهِ، فَضَرَبَ بَيْنَ ثَدْيَيَّ ضَرْبَةً خَرَرْتُ لِاسْتِي، قَالَ: ارْجِعْ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا عُمَرُ، مَا حَمَلَكَ عَلَى مَا فَعَلْتَ؟» قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، بِأَبِي أَنْتَ، وَأُمِّي، أَبَعَثْتَ أَبَا هُرَيْرَةَ بِنَعْلَيْكَ، مَنْ لَقِيَ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُسْتَيْقِنًا بِهَا قَلْبُهُ بَشَّرَهُ بِالْجَنَّةِ؟ قَالَ: «نَعَمْ»، قَالَ: فَلَا تَفْعَلْ، فَإِنِّي أَخْشَى أَنْ يَتَّكِلَ النَّاسُ عَلَيْهَا، فَخَلِّهِمْ يَعْمَلُونَ، قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَخَلِّهِمْ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 31]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance muna zaune a gefen manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, a tare damu akwai Abubakar, da Umar a cikin wasu mutane, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a tsakaninmu, sai ya ɗan jikirta mana, sai muka ji tsoron a cutar da shi ba mu sani ba, sai muka firgita, sai muka tashi, na kasance farkon wanda ya firgita, sai na fita ina neman manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har na zo wani shinge na mutanen Madina na Banu Najjar, sai na kewaye shi shin zan samu wata ƙofa gare shi ? ban samu ba, sai ga wata 'yar ƙorama tana shiga a cikin shingen daga rijiyar Kharija - rabi'u shi ne korama - sai na takure, sai na shiga wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi -, sai ya ce: "Abu Huraira" sai na ce: Eh, ya manzon Allah, ya ce: "Meke tafe da kai?" na ce: Ka kasance a tsakaninmu, sai ka miƙe, sai ka jinkirta gare mu, sai muka ji tsoron a cutar da kai bamu sani ba, sai muka firgita, sai na zama farkon wanda ya firgita, sai na zo wannan shingen, sai na takure kamar yadda dila yake takurewa, alhali waɗannan mutanen suna bayana, sai ya ce: "Ya Abu Huraira" sai ya bani takalmansa, ya ce: "Ka tafi da takalman nan waɗannan, duk wanda ka gamu da shi ta bayan wannan shingen yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa tana sakankancewa da ita, to ka yi masa albishir da aljanna", sai Umar ya zama farkon wanda ya haɗu da ni, sai ya ce: Waɗannan takalman fa ya Abu Huraira? sai na ce: Waɗannan takalman manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya aikoni da su cewa wanda na haɗu da shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita, in yi masa albishir da aljanna, sai Umar ya daki tsakanin nonuwana da hannunsa sai na faɗi ta bayana, sai ya ce: Ka koma ya Abu Huraira, sai na koma wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai na fara shesseƙin kuka, kuma Umar ya hauni, sai gashi a bayana, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Meke damunka ya Abu Huraira?" na ce: Na hadu da Umar, sai na ba shi labarin abinda ka aikoni da shi, sai ya daki tsakanin nonuwana duka da na fadi ta bayana, ya ce: Ka koma, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Umar, me yasa ka aikata haka?" ya ce: Ya Manzon Allah, fansarka babana da babata, shin ka aiki Abu Huraira da takalmanka cewa idan ya gamu da wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita ya yi masa albishir da aljanna? ya ce: Eh, ya ce: Kada ka aikata, domin cewa ni ina jin tsoron mutane su dogara a kanta, kyalesu su yi aiki, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: to ka kyalesu.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 31]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a zaune a cikin wasu jama'a cikin sahabbansa, daga cikinsu akwai Abubakar da Umar, sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe sannan ya ɗan jinkirta bai gare dawo ba, sai suka ji tsoron kada ya gamu da wani mummunan abu cikin maƙiyi; kodai ribacewa ko waninsa. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka miƙe a firgice, farkon wanda ya fara firgita shi ne Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - har ya je wata gona ta Banu Najjar, sai ya fara kewayata wataƙila ya samu wata buɗaɗɗiyar ƙofa bai samu ba, sai dai ya samu wata 'yar ɓula (kafa) ƙarama a cikin garu wacce ruwa zai shiga daga gare ta , sai ya takure jikinsa har ya shiga sai ya samu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Kaine Abu Huraira? Ya ce: Eh. Ya ce: Meke damunka? Sai Abu Huraira ya ce: Ka kasance kana cikimmu, sai ka miƙe sai kaɗan jinkirta ba mu ganka ba, sai muka ji tsoron mu rasaka, sai muka firgita, na kasance ni ne farkon wanda ya firgita, sai na zo wannan shingen, sai na yi gaggawa kamar yadda dila yake yin gaggawa, alhali waɗannan mtanen suna bayana. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi takalmansa alamar cewa shi mai gaskiya ne, kuma ya ce da shi: Ka tafi da takalman nan nawa waɗannan, duk wanda ka gamu da shi a bayan wannan shingen yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma zuciyarsa ta sakankancewa da shi; duk wanda siffarsa ta zama haka to shi yana daga cikin 'yan aljanna. Farkon wanda ya fara gamuwa da shi shi ne Umar, sai ya ce da shi: Waɗannan waɗane takalma ne ya Abu Huraira? Sai ya ce: Waɗannan takalaman manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikoni da su cewa duk wanda na gamu da shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da haka, to in yi masa albishir da aljanna. Sai Umar ya daki ƙirjin Abu Huraira da hannunsa sai ya faɗi ta bayansa, sai ya ce: Ka koma ya Abu Huraira, sai na dawo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a firgice fuskarsa ta canja yana shirin yin kuka, kuma Umar ya bini ya tafi a bayana. Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Me yasameka ya Abu Huraira? Na ce: Na gamu da Umar, sai na ba shi labarin abinda ka aikoni da shi, sai ya dakeni duka ɗaya har na faɗi ta bayana, kuma ya ce: Ka koma. Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya Umar, Me yasa ka aikata haka? Sai Uamr ya ce: Ya manzon Allah, fansarka babana da babata, shin ka aiki Abu Huraira da takalmamnka cewa wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da hakan cewa ya yi masa albishir da aljanna? Ya ce: Eh. Ya ce: To kada ka aikata, domin cewa ni ina jin tsoron kada mutane su dogara akan faɗinta kawai ba tare da aiki ba, ƙyalesu su yi aiki. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To ka ƙyalesu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tsananin soyayyar sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kwaɗayinsu akan kuɓutarsa daga dukkanin wani abin ƙi.
  2. Halaccin yin albishir da labari mai faranta rai.
  3. Imani magana ne da kuma aiki da ƙudurin zuci.
  4. Alƙali Iyadh da waninsa suka ce: Aikin Umar - Allah Ya yarda da shi da kuma bibiyar da ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai zama bijire masa da kuma yi masa raddi ba; dan abinda ya aiko Abu Huraira da shi bai zama mara daɗaɗa zukatan al'umma da kuma yi musu bushara ba, sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa ɓoye wannan ya fi maslaha garesu kuma ya fi cancanta dan kada su dogara, kuma hakan ya fi musu alheri daga gaggauto wannan albishir ɗin, lokacin da ya bijiro shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ga ya yi daidai a cikinsa.
  5. Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin shugaba da kowanne babba idan ya ga wani abu kuma wasu daga mabiyansa suka ga saɓaninsa; to cewa shi yana kamata ya bijiro shi ga wanda yake bi dan ya duba, idan ya bayyana gare shi cewa abinda mabiyin ya faɗe shi ne daidai sai ya dawo zuwa gare shi in kuma ba haka ba ya bayyanawa mabiyin amsar shubuhar da ta bijiro masa.
  6. Halaccin kamewa daga yaɗa wasu ilimummukan da ba'a buƙatuwarsu dan maslaha ko tsoron ɓarna.
  7. Bushara mai girma ga masu Tauhidi, kuma cewa wanda ya mutu alhali shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa to aljanna ta tabbata gare shi.
  8. Ƙarfin Umar - Allah Ya yarda da shi - da hikimarsa, da kuma yalwar fiƙihunsa.
  9. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa akwai halaccin shigar mutum mallakin waninsa ba tare da izininsa ba idan ya san cewa zai yarda da hakan , dan soyayyar dake tsakaninsu ko wanin haka.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin