عن أنس بن مالك رضي الله عنه:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمُعَاذٌ رَدِيفُهُ عَلَى الرَّحْلِ قَالَ: «يَا مُعَاذُ بْنَ جَبَلٍ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، قَالَ: «يَا مُعَاذُ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، ثَلَاثًا، قَالَ: «مَا مِنْ أَحَدٍ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صِدْقًا مِنْ قَلْبِهِ إِلَّا حَرَّمَهُ اللهُ عَلَى النَّارِ»، قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَفَلَا أُخْبِرُ بِهِ النَّاسَ فَيَسْتَبْشِرُوا؟ قَالَ: «إِذًا يَتَّكِلُوا». وَأَخْبَرَ بِهَا مُعَاذٌ عِنْدَ مَوْتِهِ تَأَثُّمًا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 128]
المزيــد ...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki.
Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 128]
Mu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa.
A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa.
Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta.
Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri?
Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka.
Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.