عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ وَعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«مَا يُصِيبُ الْمُسْلِمَ مِنْ نَصَبٍ وَلَا وَصَبٍ وَلَا هَمٍّ وَلَا حُزْنٍ وَلَا أَذًى وَلَا غَمٍّ حَتَّى الشَّوْكَةِ يُشَاكُهَا إِلَّا كَفَّرَ اللهُ بِهَا مِنْ خَطَايَاهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5641]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Alkhudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5641]
Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa abinda musulmi yake samu na cutuka da bakin cki da takaici da masibu da tsanani da tsoro da yunwa - kai koda akwai kayar da za ta taba shi ta sashi radadi -, hakan zai zama kaffara ga zunubansa da kuma kankare kurakuransa.