عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«حُجِبَتِ النَّارُ بِالشَّهَوَاتِ، وَحُجِبَتِ الْجَنَّةُ بِالْمَكَارِهِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6487]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6487]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wuta abar kewayewace da al'amuran da rai take son sha'awrsu na aikata abubuwan da aka haramta, ko takaitawa a wajibai; Duk wanda ya bi son ransa a hakan to ya cancanci wuta, Kuma cewa Aljanna abar kewayewace da al'amuran da rai take kin su; kamar lazimta akan abubuwan da aka umarta da barin abubuwan da aka haramta, da hakuri akan hakan, idan ya kutsa kuma ya yaki ransa a hakan to ya cancanci shiga Aljanna.