عن ابن مسعود رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم:
«الْجَنَّةُ أَقْرَبُ إِلَى أَحَدِكُمْ مِنْ شِرَاكِ نَعْلِهِ، وَالنَّارُ مِثْلُ ذَلِكَ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6488]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6488]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa aljanna da wuta suna kusa da mutum kamar kusancin igiyar takalmin da yake kasancewa akan bayan kafa, domin kuwa mutum zai iya aikata wani aikin biyayya na yardar Allah - Mai girma da daukaka - da zai shiga aljanna da shi, ko sabon da zai zama sababi na shiga wuta.