عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الدُّنْيَا سِجْنُ الْمُؤْمِنِ وَجَنَّةُ الْكَافِرِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2956]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2956]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa rayuwar duniya ga mumini kamar kurkuku ce dan wajibci ga abubuwan da shari'a da aka ɗora masa, na aikata abinda aka yi umarni da shi da kuma barin abinda aka yi gargaɗi da shi, idan ya mutu ya huta daga wannan kuma zai koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya. ita (duniyar) kamar kuma aljanna ce ga kafiri; domin cewa shi yana aikata dukkanin abinda ransa yake sha'awarsa kuma son ransa yake umartarsa, idan ya mutu zai juya zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yimasa tanadi a ranar alƙiyama na azaba tabbatacciya.