Karkasawa: Falaloli da Ladabai .

عن أبي الدرداء رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ رَدَّ عَنْ عِرْضِ أَخِيهِ رَدَّ اللهُ عَنْ وَجْهِهِ النَّارَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».

[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 1931]
المزيــد ...

Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce:
"Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".

[Ingantacce ne] - [Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi] - [Sunan Tirmizi - 1931]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa musulmi a bayan idonsa ta hanyar hana zarginsa ko munana masa, to, lallai Allah Zai kareshi daga azaba a ranar al-ƙiyama.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga magana a kan mutuncin musulmai.
  2. Sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki, wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kareshi daga wuta.
  3. Musulunci addinin 'yan uwantaka ne da taimakekeniya a tsakanin ma'abotansa.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)