+ -

عن جابر رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«رَحِمَ اللهُ رَجُلًا سَمْحًا إِذَا بَاعَ، وَإِذَا اشْتَرَى، وَإِذَا اقْتَضَى».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2076]
المزيــد ...

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2076]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da rahama ga dukkanin wanda ya kasance mai sauki mai kyauta a cinikinsa; Ba ya tsanantawa mai saye a farashinta kuma yana mu'amalantarsa da kyakkyawan halaye, Mai sauki mai kyauta idan zai siya, baya tauye mudu kuma ba ya karanta daga kimar haja. Mai sauki mai kyauta idan ya nemi biyan basukansa; ba ya tsanantawa akan talaka da mabukaci, kai yana nemansa da sauki, kuma yana jinkirtawa wanda ke cikin mawuyacin hali.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأكانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Daga manufofin shari'a akwai kiyaye wa akan abinda yake gyara alakoki tsakanin mutane.
  2. Kwadaitarwa a aiki da kyawawan halaye a ciki da mu'amaloli tsakanin mutane na siye da siyarwa da makamancin hakan.