+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ»، قِيلَ: مَنْ؟ يَا رَسُولَ اللهِ قَالَ: «مَنْ أَدْرَكَ أَبَوَيْهِ عِنْدَ الْكِبَرِ، أَحَدَهُمَا أَوْ كِلَيْهِمَا فَلَمْ يَدْخُلِ الْجَنَّةَ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2551]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2551]

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ƙasƙanci da taɓewa har saida hakan ya kai, kai ka ce ya ɗora hancinsa a cikin ƙasa - ya maimaitata sau uku - sai aka tambaye shi: Waye wannan ya manzon Allah wanda ka yi mummunar Addu’a akansa?
Sai (Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata aagre shi - ya ce: Wanda ya riski mahaifansa a lokacin tsufa - ɗayansu ko su biyun -, ba su zama sababi na shigarsa aljanna ba; hakan saboda rashin kyautata musu da kuma saɓa musu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin biyayya ga mahaifa, kuma hakan yana daga sabubban shiga aljanna, musamman ma a lokacin tsufansu da rauninsu.
  2. Saɓawa iyaye yana daga manyan zunubai.