عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسِيرُ فِي طَرِيقِ مَكَّةَ، فَمَرَّ عَلَى جَبَلٍ يُقَالُ لَهُ جُمْدَانُ، فَقَالَ: «سِيرُوا هَذَا جُمْدَانُ، سَبَقَ الْمُفَرِّدُونَ» قَالُوا: وَمَا الْمُفَرِّدُونَ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الذَّاكِرُونَ اللهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2676]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce wani dutse ana ce masa Jumdan, sai ya ce: "Ku tafi ! wannan Jumdan ne,Masu kaɗaitawa sun rigaya" Suka ce: Suwaye musu kaɗaitawa ya manzon Allah? ya ce: "Masu ambatan Allah da yawa maza da mata masu ambatan Allah".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2676]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana matsayin masu ambatan Allah da yawa, kuma cewa su sun kaɗaita kuma sun riga wasunsu da samun manyan darajoji acikin aljannar ni'ima, kuma ya kamantasu da dutsen Jumdan wanda shi kadai ne babu irinsa a cikin duwatsu.