Karkasawa: Falaloli da Ladabai .
+ -

عن أبي أيوب الأنصاري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«لَا يَحِلُّ لِرَجُلٍ أَنْ يَهْجُرَ أَخَاهُ فَوْقَ ثَلَاثِ لَيَالٍ، يَلْتَقِيَانِ، فَيُعْرِضُ هَذَا وَيُعْرِضُ هَذَا، وَخَيْرُهُمَا الَّذِي يَبْدَأُ بِالسَّلَامِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6077]
المزيــد ...

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6077]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi hani game da ƙauracewar musulmi ga ɗan uwansa musulmi sama da dare uku, kowane ɗaya daga cikinsu zai haɗu da ɗayan, amma ba zai yi masa sallama ba, kuma ba zai yi masa magana ba.
Mafificin waɗannan masu husumar biyun shi ne wanda zai yi ƙoƙarin gusar da ƙauracewar, kuma ya fara yin sallama, abin nufi da ƙauracewa a nan shi ne na son rai, amma kauracewa saboda haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - kamar ƙauracewa masu saɓo da 'yan bidi'a da mugayen abokai, to, wannan ba a iyakanceshi da wani lokaci, kawai ya na rataya ne da maslaha a ƙauracewar, kuma yana gushewa da gushewarta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin ƙauracewa na kwana uku, da ƙasa da hakan, don kula da ɗabi'un mutane, sai akayi afuwa a kan ƙauracewa a cikin kwana uku har wannan abin da ya bijirowar ya tafi.
  2. Falalar sallama, kuma tana gusar da abin da ke cikin zukata, kuma alama ne a kan soyayya.
  3. Kishin musulunci a kan 'yan uwantaka da sabo a tsakanin ma'abotansa.