عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «الصلوات الخمس، والجمعة إلى الجمعة، ورمضان إلى رمضان مُكَفِّراتٌ لما بينهنَّ إذا اجتُنبَت الكبائر».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga manzon Allah SAW ya ce: "Salloli Biyar, da jumu'a zuwa Jumu'a, da Ramadan zuwa ramadan suna kankare abunda yake tsakaninsu (Na Zunubai) idan aka nisanci Manyan laifuka"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]
Sallaoli Biyar suna kankare Zunuban dake tsakaninsu na Zunubai sune qananan zunubai sai dai Manyan Zunubai basa kankaresu sai an tuba, kuma haka Sallar Jumu'a zuwa wacce take binta, haka na Azumin Watan Ramadan zuwa wani Azumin da yake gabansa.