عن خَولة الأنصاريةِ رضي الله عنها قالت: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول:
«إِنَّ رِجَالًا يَتَخَوَّضُونَ فِي مَالِ اللهِ بِغَيْرِ حَقٍّ، فَلَهُمُ النَّارُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 3118]
المزيــد ...
Daga Khaulat Al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3118]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labari game da wasu mutane da suke tasarrufi a dukiyoyin musulmai da ɓarna, suna ɗaukarsu ba tare da wani haƙƙi ba, wannan ma'ana ce mai gamewa game da dukiya ta hanyar tara ta da kasuwanci da ita ba tare da halaccinta ba, da ciyar da ita ba ta ingantacciyar hanya ba, cin dukiyoyin marayu da dukiyoyin waƙafi da musanta amanoni da ƙwace ba tare da cancanta ba daga dukiyoyi game gari, to, duk suna shiga cikin wannan.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da labarin cewa sakamakonsu (shi ne) wuta a ranar al-ƙiyama.