عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ اللهَ مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2742]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2742]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa duniya mai zakice a abubuwan zaki, kuma koriya a abin gani, sai mutum ya rudu da ita ya yi zari a cikinta ya kuma sanya ta mafi girman himmarsa. Kuma cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ya sanya shashinmu zai maye gurbin sashi a wannan duniyar, dan ya duba ya zamu yi aiki, shin zamu tsaya da biyayyarSa, ko zamu saba maSa? Sannan ya ce: Ku kiyayi jin dadin duniya ya rudeku da kawarta, sai ya doraku akan barin abinda Allah Ya umarceku da shi, da kuma afkawa a cikin abinda ya haneku daga gareshi. Daga mafi girman abinda ya wajaba a kiyaya daga gare shi daga fitintinun duniya (su ne) mata, cewa ita ce farkon fitinar da Banu Isra'ila suka afka a cikinta.