عن عائشة رضي الله عنها قالت: سمعتُ من رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول في بيتي هذا:
«اللَّهُمَّ مَنْ وَلِيَ مِنْ أَمْرِ أُمَّتِي شَيْئًا فَشَقَّ عَلَيْهِمْ فَاشْقُقْ عَلَيْهِ، وَمَنْ وَلِيَ مِنْ أَمْرِ أُمَّتِي شَيْئًا فَرَفَقَ بِهِمْ فَارْفُقْ بِهِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1828]
المزيــد ...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana faɗa a cikin wannan ɗakin nawa :
"Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1828]
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi mummunar addu'a a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani al'amari daga al'amuran musulmai ya kasance ƙarami ne ko babba, kuma duk ɗaya ne, wannan shugabancin ya zama shugabanci ne mai gamewa, ko wani bangare ne keɓantacce, kuma ya shigar musu da tsanani bai tausasa musu ba, cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa sakayya daga jinsin aikinsa ta yadda zai tsananta masa.
Kuma cewa duk wanda ya tausasa musu ya sauƙaƙa al'amuransu cewa Allah Zai tausasa masa kuma zai sauƙaƙa al'amuransa.