عن مَعقِلِ بن يَسار المُزَنِيّ رضي الله عنه قال: إني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«مَا مِنْ عَبْدٍ يَسْتَرْعِيهِ اللهُ رَعِيَّةً، يَمُوتُ يَوْمَ يَمُوتُ وَهُوَ غَاشٌّ لِرَعِيَّتِهِ، إِلَّا حَرَّمَ اللهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 142]
المزيــد ...
Daga Ma'aƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 142]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ba da labarin cewa kowane mutumin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanyashi majiɓinci, kuma shugaba ga mutane, duk ɗaya ne ya kasance shugabanci ne mai gamewa kamar sarki, ko keɓantaccen shugabanci ne kamar mutum a gidansa da mace a gidanta, sai ya gaza a haƙƙin waɗanda aka ba shi kiwonsu, ya yi musu algus bai yi musu nasiha ba, sai ya tozarta haƙƙoƙinsu na addini da na duniya, to, haƙiƙa ya cancanci wannan uƙubar mai tsanani.