lis din Hadisai

Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu*. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.
عربي Turanci urdu
"Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi*" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".
عربي Turanci urdu
"Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".
عربي Turanci urdu
"Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".
عربي Turanci urdu
"Addini nasiha ne*" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
عربي Turanci urdu
"Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa".
عربي Turanci urdu
"Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".
عربي Turanci urdu
"Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya*, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
عربي Turanci urdu
Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari. Sai ya ce: '@Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu*, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
عربي Turanci urdu
"Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".
عربي Turanci urdu
Ka bauta wa Allah shi kaxai, kada ka hada kome da Shi, kuma ka bar abin da ubanninka suka fada, kuma Ya umurce mu da yin addu’a da gaskiya
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila
عربي Turanci urdu
"Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa*, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".
عربي Turanci urdu
ku rika zantar da Mutane da abinda suka sani, ko kuna son su karyata Allah da manzonsa ne
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi".
عربي Turanci urdu
"Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta*, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".
عربي Turanci urdu
"Bawa ba zai taba kaiwa Matakin Masu tsoron Allaba har sai ya bar abunda babu laifi a cikinsa
عربي Turanci urdu
Ka yi haquri, domin babu wani lokaci da zai zo face bayan hakan akwai wani sharri a bayansa har sai ka hadu da Ubangijinka
عربي Turanci urdu
Ya Annabin Allah, shin kana ganin idan muna da wasu shugabanni da suke tambayarmu haƙƙinsu kuma suna hana mu hakkokinmu, to me zaka umarcemu? sai ya kauda kai, sannan ya tambaye shi, sai ya kauda kai, sannan ya tambaye shi a karo na biyu ko karo na uku, sai al-Ash'as ɗan Ƙais ya fizgo shi, ya ce:@"Ku ji, kuma ku bi, kaɗai abinda aka ɗora musu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku yana kanku".
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya yi mubaya'a ga limami kuma ya ba shi cinikin hannunsa da 'ya'yan zuciyarsa, to ya rantse da shi idan zai iya.
عربي Turanci urdu
Wanene daga cikinku ya yi amfani da shi don aiki, kuma mun kasance muna nannade a dinka, da abin da ke sama da shi, zaren da zai zo da shi ranar tashin kiyama
عربي Turanci urdu
"Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto*, ku yi bushara, ku nemi taimakon Allah da jijjifi da kuma yammaci da wani abu na duhun dare".
عربي Turanci urdu
"Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,* shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".
عربي Turanci urdu
Na Hore ku da ji da kuma biyayya cikin Matsuwarka da kuma Yalwatarka, da cikin jin dadi da kuma rashin jin dadinka
عربي Turanci urdu
Mun kasance Muna yiwa Annabi SAW Mubaya'a kan ji dabiyayya, yana cewa da mu cikin abunda zaku iya
عربي Turanci urdu
Yana kan mutum musulmi ji da kuma da’a a cikin abin da yake so ko yake ki sai dai in an umarce shi da sabo, to idan an umarce shi da sabo to babu ji kuma babu da’a, kuma ya ce kadai ana da’a ne a cikin abin da shari ta san da shi
عربي Turanci urdu
"Duk wanda ya wulakanta Shugaba to Allah sai ya Wulakanta shi"
عربي Turanci urdu
Kuji kuma Kub,i koda kuwa kuwa Bawa Bahabashe aka Shugabantar muku, Kai kace kansa gudaddajin Zabibi ne
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun
عربي Turanci urdu
Mafiyan Shuwagabanninku su ne wadan da kuke son su kuma suma suke sonku, kuke sadawa da su kuma suma suke saduwa, Mafi Sharrin Suwagabannninku su ne wadanda kuke kinsu suke kinku, kuke La'antarsu suma suna la'antarku
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW ya hana duka a fuska, da shaushawa a Fuska
عربي Turanci urdu
"Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta".
عربي Turanci urdu
Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, @Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
عربي Turanci urdu
Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "@Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su*, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
عربي Turanci urdu
"Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi*, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".
عربي Turanci Indonisiyanci
Ya kai Abdurrahman Dan Samra, Kada ka nemi Mulki, sabida Idan aka baka sabida kai ka nema to sai abarka da ita
عربي Turanci urdu
Idan Allah yana son yarima mai kyau, ka sanya shi Ministan Ikhlasi, cewa ya manta an ambata, amma ya ce ya taimake shi, kuma idan yana so ya yi in ba haka ba ya sanya shi rashin lafiya, idan ya manta bai ambaci ba, amma ya ce ba Aanh
عربي Turanci urdu
Allah bai aiko daga annabi ba, kuma ban sanya wanda zai gaje shi ba daga khalifa, amma yana da layi biyu: layin da yake umurtar shi da yi masa nasiha zuwa ga alheri, kuma layin da yake umartar shi da sharri da kwadaitarwa
عربي Turanci urdu
"Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi*, lokacin da ya girma, sai ya cewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zai zo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan ya zo wajen matsafin sai ya dake shi, sai ya kai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce : Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce: Matsafi ne ya tsareni. Yana cikin haka sai ga shi ya zo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko mai ibada ne ya fi ? sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shi ne mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance ya ji, sai ya zo masa da kyaututtuka masu yawa, sai ya ce: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka yi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yana zama, sai sarkin ya ce da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? ya ce: Ubangijina kuma Ubangijinka Shi ne Allah, sai ya kama shi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har saida ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka ya kai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai aka zo da mai ibadar sai aka ce masa: Ka bar Addinika, sai ya ƙi, sai ya sa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi har saida ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da ɗan majalisar sarki sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai aka ɗora zarton akan tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da yaron sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai ya miƙa shi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan ya bar Addininsa to (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗauke shi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa to inba haka ba fa to ku jefa shi, sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiye, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya cewa sarkin: Kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, ya ce: Menene shi? ya ce: Ka tara mutane wuri ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, sai ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, sai aka zo wa sarkin sai aka ce da shi: Shin kana ganin abinda tsoro, haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sun yi imani, sai ya yi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko a ce masa: Ka faɗa sai suka aikata, har sai da wata mace ta zo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".
عربي Turanci urdu
Ya Abu Dharr, na gan ka mai rauni, kuma ina son ka abin da nake so wa kaina, kar ka dora wa mutum biyu, kuma kar ka karbi kudin maraya
عربي Turanci urdu
Ya Abu Dharr, kai mai rauni ne, kuma amana ce, kuma a ranar lahira abin kunya ne da nadama, sai dai wadanda suka karbe ta da hakkinta suka biya abin da ke kanta.
عربي Turanci urdu
Na ambaci wani abu game da adalcinmu, kuma ina tsammanin zai kulle ni, don haka na ba da umarnin a raba shi
عربي Turanci urdu
Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi*, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».
عربي Turanci urdu
Kada Ku haxani da Allah a wajen roqona,na rantse da Allah babu wanda zai tanbayeni daga cikinku wani abu sai inbasashi abunda ya roqa ina kuma ina mai fushi da shi, kuma Allah ya sanya Masa Al-barka cikin abunda na bashi
عربي Turanci urdu
Idan Dayankuya tashi cikin dare, sai ya Harshensa ya fara Nauyi wajen karanta Kur'ani, bai san mai yake Karantawa ba to ya Kwanta
عربي Turanci urdu
Lallai Allah yayi Umarni ga Manzonsa kuma baiyi Umarni ga ku ba, kuma nima din anyi mun Izinin wani lokaci ne na rana kawai, kuma wannan Haramcin ya dawo bayan nan yau kamar yadda Haramcin yake a jiya. to wanda yaji ya gayawa wanda baiji ba.
عربي Turanci urdu
Ina tafiya tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a kansa tare da dusar kankara mai kauri a cikin dutsen.
عربي Turanci urdu
"Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, @Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira*, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
عربي Turanci urdu
"Kaji Tsoron Allah cikin wadan nan Dabbobin da basa Magana, saboda ku hau su suna lafiya, kuma kuci (Namansu) Lafiya
عربي Turanci urdu
"Manzon Allah ya Kasance, yana jinkirtawa a bayan Matafiya, Saboda ya taimakawa Rarrauna, Kuma ya dauke shi kuma yayi Masa Addu'a"
عربي Turanci urdu
Mu muna shiga ga Shugabanninmu sau Mu gaya musu Sacanin abunda Muke faca idan muka futo daga Wurinsu, sai ya ce: Mu muna qirga wannan cikin Munafunci a lokacin Manzon Allah SAW
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzo da wani Mutum sai aka ce da shi: Wannan wane ne gemunsa yana xigar giya, sai ya ce: Mu an hana mu bi kwakwaffi, kuma sai dai in wani abu ya bayyana a gare mu sai muyi riqo da shi
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- ya hanatsaure hantsar Dabbobi
عربي Turanci urdu
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin tafiya, sai ya tafi wata buƙatarsa, sai muka ga wata tsuntsuwa tare da 'yayanta biyu, sai muka ɗauke su, sai tsuntsuwar ta zo tana fakan-fakan (tana nemansu), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Waye ya raba wannan da ɗanta? ku maida mata da ɗanta», kuma sai ya ga wasu ramin tururuwa wanda muka ƙona shi, sai ya ce: «‌Waye ya ƙona wannan?» mukace: Mune. Ya ce: @«‌Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta».
عربي Turanci urdu
Ganin cewa kare na zaune a cikin kududdufi, kuma kusan kishirwa ta kashe shi, lokacin da wata karuwa ta ganta a matsayin karuwa ga Banu Isra'ila, don haka ta firgita da shi.
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Bata baccin dare! @Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce ginin masallatai a cikin gidaje, kuma a tsaftace sh
عربي Turanci urdu
ina rokonka da girman Allah shin kaji Manzon Allah - SAW- yana cewa: Ka amsa mini, Ya Allah ka tallafa masa da Ruhu Mai Tsarki? Ya ce: Ey, haka ne.
عربي Turanci urdu
«‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
عربي Turanci Indonisiyanci
Idan kudin Bahrain suka zo, zan ba ka haka da sauransu da sauransu
عربي Turanci urdu
Ya Amirul Muminina, Allah Madaukaki ya ce wa Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Ka yi afuwa ka yi umarni da al'ada kuma ka kau da kai daga jahilai.
عربي Turanci urdu
NASA an dauki wahayi ne a zamanin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma wannan wahayi ya daina, amma Nokhzkm yanzu ya hada da dawo mana daga kasuwancinku, ya nuna mana kyau Omnah da Qrbnah, ba mu asirin wani abu ba, Allah ya yi masa hisabi a cikin sirrinsa, kuma ya nuna mana Bad ba mu gaskata shi ko gaskata shi ba
عربي Turanci urdu
"Mafi Al-kairin Sahabbai guda hudu ne, Mafi Al-khairin Saraya kuma guda Dari hudu, kuma mafi Al-kairin Rundunar yaki Dari Hudu, Kuma ba za'a taba rinjayar Dubu goma Sha biyu ba daga 'yan Kadan"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW ya ga wani jaki an masa zanen wuta a fuskarsa, sai ya Musanta hakan
عربي Turanci urdu
Kun ganni na bakwai a cikin Bakwai Bakwai. Ba mu da wani bawa sai wanda ya mari karaminmu, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da 'yantar da ita
عربي Turanci urdu
«Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu,* ku saurara idan suka sauka ko suka faru wanda yake da raƙuma to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakai to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa to ya risku da ƙasarsa», ya ce sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah to kana ganin wanda ba shi da raƙuma ko tumakai ko ƙasa fa? ya ce: «Ɗayanku ya nufi takobinsa sai ya caka tsinin takobin a dutse, sannan ya tsira idan zai iya tsira, ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar?». Ya ce: sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan aka tilastani har aka tafi da ni zuwa daya daga jama'a biyun, ko daya daga bangarori biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo sai ta kasheni? ya ce: "Zai koma da zunubinsa da kuma zunubinka, kuma ya zama daga 'yan wuta".
عربي Turanci Indonisiyanci