عن أبي شُريح -خُوَيْلِدِ بن عمرو الخُزَاعي العدوي رضي الله عنه-: أنه قال لعمرو بن سعيد بن العاص -وهو يبعث الْبُعُوثَ إلى مكة- ائْذَنْ لي أيها الأمير أن أُحَدِّثَكَ قولا قام به رسول الله صلى الله عليه وسلم الغد من يوم الفتح؛ فسمعَتْه أُذُنَايَ ، وَوَعَاهُ قلبي، وأبصرته عيناي حين تكلم به أنه حمد الله وأثنى عليه، ثم قال: «إن مكة حَرَّمَهَا الله تعالى، ولم يُحَرِّمْهَا الناس، فلا يحل لِامْرِئٍ يؤمن بالله واليوم الآخر: أن يسفك بها دمًا، ولا يعضد بها شجرة، فإن أحد ترخص بقتال رسول الله صلى الله عليه وسلم فقولوا: إنَّ الله أذِن لرسوله ولم يأذن لكم. وإنما أذِنَ لي ساعة من نهار، وقد عادت حُرْمَتُهَا اليوم كَحُرمتها بالأمْسِ، فَلْيُبْلِغِ الشَّاهِدُ الغائب». فقيل لأبي شريح: ما قال لك؟ قال: أنا أعلم بذلك منك يا أبا شريح، إن الحرم لَا يُعِيذُ عاصيا، وَلَا فَارًّا بدمٍ، ولَا فَارًّا بِخَرْبَةٍ.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Shuraih Khuwailid Dan Amr Alkhuza'i Al'adawi cewa ya ce da Amr Dan Sa'id Dan Asw kuma shi yana aika yan aike zuwa Makka kayi mun izini ya kai wannan Jagora kan in gaya maka wata Magana da Annabi ya yi ta washe garin bude Makka; sai naji shi yana cewa da kunnuwa na, kuma zuciya ta ta rike mai ya fada kuma ina ganinsa lokacin da yake fadar: cewa shi ya godewa Allah kuma yabi Ubangiji sannan ya ce: Lallai Makka Allah ya Haramta ta kuma amma Mutane basu Haramta ta ba, to bai halatta ga Mutum ba yayi Imani da Allah da kuma Ranar Lahira, ya zubda jini a cikinta, ko kuma ya sare bishiyarta, to idan wani ya kafa dalili da yakin Annabi to kuce: Lallai Allah ya yi Masa Izini ne kuma ku bai muku ba, kuma cewa anyimun Izini ne dan wani lokaci na rana kuma bayan nan haramcin ya dawo kamar haramcinsa jiya to duk wanda yaji ya gayawa wanda baiji ba to akace da Abu Shuraih: Mai ya ce Maka? Ina sane da wannan sama da kai Kai Abu Shuraih, Lallai cewa Harami baya bada kariya ga mai sabo, ko kuma Mutumin da ya gudo cikinsa bayan yayi kisa, ko kuma ya gudo bayan yayi barna.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Kuma yayin da Amr Dan Sa'ad Da Asw, wanda aka fi sani da Al'ashdaq, cewa ya shirya runduna zuwa Makka Mai Alfarma kuma a lokacin yana sarki ne a Madina don ya yaki Abdullahi Dan Zubair sai Abu Shuraih ya zo masa, Khuwailid Dan Amr Alkhuza'i, don yayi masa Nasiha kan hakan. to sabida kasancewar wanda za'a yi wa nasihar yanajin kansa sai Abu Shuraih ya tausasa murya a gares hi, don Hikimarsa da kuma dora shi kan daidai don Nasihar tasa ta samu gurbin karba, da kuma karshen yayi kyau, sai ya nemi ayi masa ison ganin nasadon yi masa Nasiha a al'amarin kan rundunar da zzai aika, kuma ya bashi labarin cewa shi yana da tabbacin abinda zai gaya masa, kuma ya kafa dalili da cewa shi yaji wannan abu ne da kunnensa kuma ya rike shi a cikin zuciyarsa, kuma idonsa yaga lokacin da Annabi yake fadarsa, sai Amr Dan Sa'id yayi masa izinin yin Magana. Sai Abu Shuraih ya ce: Lallai cewa Annabi a Safiyar ranar bude makka ""cewa shi ya godewa Allah kuma yabi Ubangiji sannan ya ce: Lallai Makka Allah ya Haramta taTun lokacin da ya halicci sammai da kasa" kuma tana nan a girmamae da kuma tsarkinta, kuma amma mutane basu haramta ta ba kamar yadda suka haramta makiyaya wacce take ta dan wani lokaci ba da kuma wurin kiwo da shan ruwan dabbobi, kuma cewa Allah ne da kansa ya jibanci Haramtawar, don ya kasance mafi girma da kuma isa wajen haramcin to idan idan haramcin ya kasance tsoho haka kuma daga Allah ya ke to bazai halatta ga wani Mutum ba da yayi imani da Allah da kuma ranar lahira kuma indai yana kishin Imaninsa ya zubar da da Jini ko kuma ya sare bishiyarta, kuma idan wani wani yai iinin yaki na a ranar bude Makka, to ai shi ba kamar Manzon Allah ba ne, kuma shi anyi masa Izini amma kai ai ba'a maka ba.kuma cewa lallai ai bai halatta a Yaketa ba ko yaushe, kuma hakan ma ya faru ne wani Dan lokaci na rana sabida waccan bukatar, kuma haramcinta ya kuma dawowakamar yadda yake to duk wanda yaji ya gayawa wanda baiji ba, don wannan ne ya kai wannan Sarki nake isar maka da wannan sakon don ni sheda ne akan wannan Maganar, safiyar Ranar bude Makkah kuma kai baka nan akai, Sai Mutane suka ce Da Abu Shuraih :dame ya amsa maka Amr din ?sai ya ce ya amsamun da cewa "Nafi ka Sanin Wannan Kai Abu Shuraih , Lallai cewa ai Harami baya Kare Mai laifi, ko kuma wanda ya gudo cikinsa bayan yayi barna" Taisir Allam (Shafi na:381) da Tanbih Al'afham (3/519,510) da kuma Ta'asisu Al'ahkam.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin
Kari