عَنْ حُذَيْفَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّهَا سَتَكُونُ أُمَرَاءُ يَكْذِبُونَ وَيَظْلِمُونَ، فَمَنْ صَدَّقَهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَأَعَانَهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَلَيْسَ مِنَّي، وَلَسْتُ مِنْهُ، وَلَا يَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ، وَمَنْ لَمْ يُصَدِّقْهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَلَمْ يُعِنْهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَهُوَ مِنِّي، وَأَنَا مِنْهُ، وَسَيَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ».
[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 23260]
المزيــد ...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".
[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 23260]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shagabanni da zasu shugabanci mutane bayan rasuwarsa zasu dinga ƙarya a magana sai su dinga faɗin abinda ba sa aikatawa, kuma suna zalinci a cikin hukunci, wanda ya shiga gurinsu ya gasgata su akan ƙaryarsu, kuma ya taimakesu da aikata zalinci ko faɗarsa, kamar ba su fatawa dan neman kusancinsu da kwaɗayin abinda ke hannunsu; to ni babu ruwana da shi, ba shi ba ni, ba ni ba shi, kuma ba zai zo Alkausara ba ranar alƙiyama. Wanda bai shige su ba , kuma bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to yana tare da ni, kuma zai zo Alkausara ranar alƙiyama ba.