عَنْ وَائِلٍ الْحَضْرَمِيِّ قَالَ: سَأَلَ سَلَمَةُ بْنُ يَزِيدَ الْجُعْفِيُّ رضي الله عنه رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ:
يَا نَبِيَّ اللهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ قَامَتْ عَلَيْنَا أُمَرَاءُ يَسْأَلُونَا حَقَّهُمْ وَيَمْنَعُونَا حَقَّنَا، فَمَا تَأْمُرُنَا؟ فَأَعْرَضَ عَنْهُ، ثُمَّ سَأَلَهُ، فَأَعْرَضَ عَنْهُ، ثُمَّ سَأَلَهُ فِي الثَّانِيَةِ أَوْ فِي الثَّالِثَةِ، فَجَذَبَهُ الْأَشْعَثُ بْنُ قَيْسٍ، وَقَالَ: «اسْمَعُوا وَأَطِيعُوا، فَإِنَّمَا عَلَيْهِمْ مَا حُمِّلُوا، وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1846]
المزيــد ...
Daga Wa'il AlHadrami ya ce: Salamatu ɗan Yazid al-Ju'ufi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce:
Ya Annabin Allah, shin kana ganin idan muna da wasu shugabanni da suke tambayarmu haƙƙinsu kuma suna hana mu hakkokinmu, to me zaka umarcemu? sai ya kauda kai, sannan ya tambaye shi, sai ya kauda kai, sannan ya tambaye shi a karo na biyu ko karo na uku, sai al-Ash'as ɗan Ƙais ya fizgo shi, ya ce:"Ku ji, kuma ku bi, kaɗai abinda aka ɗora musu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku yana kanku".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1846]
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da shugabannin da suke neman haƙƙinsu daga mutane na ji da biyayya, kuma suna hana haƙƙin da ke kansu; na yin adalci da bada ganima da dawo da abubuwan da aka zalinta da daidaito, to me zaka umarcemu mu aikata tare da su?
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kau da kai; kamar ya ƙyamaci waɗannan tambayoyin, sai dai mai tambayar ya sake maimaita masa karo na biyu da na uku, sai al-Ash'as ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya fizgo mai tambayar dan ya sa shi ya yi shiru.
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa, ya ce: Ku ji abinda suke faɗa, kuma Ku bi umarninsu; kaɗai abinda aka ɗora musu na adalci da bawa talakawa hakkinsu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku na biyayya da bada haƙƙoƙi da haƙuri akan masifu yana kanku.