+ -

عن عُبَادَةَ بن الصَّامتِ رضي الله عنه قال:
بَايَعْنَا رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم على السَّمْعِ وَالطَّاعَةِ فِي الْعُسْرِ وَالْيُسْرِ، وَالْمَنْشَطِ وَالْمَكْرَهِ، وعلى أَثَرَةٍ علينا، وعلى أَلَّا نُنَازِعَ الْأَمْرَ أهلَه، وعلى أَنْ نَقُولَ بِالْحَقِّ أينما كُنَّا، لا نَخَافُ في الله لَوْمَةَ لَائِمٍ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1709]
المزيــد ...

Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1709]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. [Kyakkyawan] sakamakon ji da bi ga majiɓinta al'amura shi ne haɗuwar kan musulmai da watsar da rarrabuwa.
  2. Wajabcin ji da bi ga majiɓinta al'amura in ba a saɓon Allah ba ne a cikin sauƙi da tsanani, da farin ciki da baƙin ciki da babakeren da za su yi.
  3. Wajabcin faɗin gaskiya a duk inda muke, ba tare da mun ji tsoron zargin mai zargi ba cikin [al'amarin] Allah