+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال:
«مَنْ ‌خَرَجَ ‌مِنَ ‌الطَّاعَةِ، وَفَارَقَ الْجَمَاعَةَ فَمَاتَ، مَاتَ مِيتَةً جَاهِلِيَّةً، وَمَنْ قَاتَلَ تَحْتَ رَايَةٍ عِمِّيَّةٍ، يَغْضَبُ لِعَصَبَةٍ، أَوْ يَدْعُو إِلَى عَصَبَةٍ، أَوْ يَنْصُرُ عَصَبَةً، فَقُتِلَ، فَقِتْلَةٌ جَاهِلِيَّةٌ، وَمَنْ خَرَجَ عَلَى أُمَّتِي، يَضْرِبُ بَرَّهَا وَفَاجِرَهَا، وَلَا يَتَحَاشَى مِنْ مُؤْمِنِهَا، وَلَا يَفِي لِذِي عَهْدٍ عَهْدَهُ، فَلَيْسَ مِنِّي وَلَسْتُ مِنْهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1848]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1848]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya fita daga biyayyar majiɓinta al'amura, kuma ya rabu da jama'ar musulunci wacce ta haɗu a kan caffar (mubaya’a) shugaba, sai ya mutu a kan wannan halin na rabuwa da rashin biyayya, to, ya mutu irin mutuwar 'yan Jahiliyya, waɗanda ba sa bin wani shugaba, kuma ba sa tarowa zuwa jama'a ɗaya, kawai sun kasance ƙungiyoyi da jama'a-jama'a da sashinsu yana yaƙar sashi.
Cewa shi ya ce: (Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin tutar da ba a fayyace gaskiyarta daga ƙaryarta ba, yana fushi saboda tsantsar ƙanilanci ga mutanensa ko ƙabilarsa, ba don taimakon Addini ko gaskiya ba, sai ya yi yaƙi don ƙabilanci ba tare da basira ko ilimi ba, to, idan aka kasheshi a kan wannan halin, ya zama kamar kisan Jahiliyya.
Kuma wanda ya yi fito na fito da al'ummarsa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kulawa da abin da yake aikatawa kuma ba ya jin tsoron uƙubarsa na kashe mumininta, kuma ba ya cika alƙawari ga ma'abota alƙawari daga cikin kafirai ko majiɓinta al'amura sai dai ma yana warwaresu, to, wannan yana daga manyan zunubai, wanda ya aikata shi, to, haƙiƙa ya cancanci wannan narkon mai tsanani.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Biyayya ga shugabanni wajiba ce a abinda ba saɓon Allah ba.
  2. A cikinsa akwai gargaɗi mai tsanani ga wanda ya fita daga biyayyar shugaba, kuma ya rabu da jama'ar musulmai, idan ya mutu a kan wannan halin, to, ya mutu a kan tafarkin ma'abota Jahiliyya.
  3. A cikin Hadisin akwai hani game da yaƙi don ƙabilanci.
  4. Wajabcin cika alƙawarurra.
  5. A cikin biyayya da lazimtar jama'a akwai alheri mai yawa, da aminci da nutsuwa, da gyara halaye.
  6. Hani daga kamanceceniya da halayen ma'abota Jahiliyya.
  7. Umarni da lazimtar jama'ar musulmai.