عَنْ بَهْزِ بْنِ حَكِيمٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ قَالَ:
قُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: مَنْ أَبَرُّ؟ قَالَ: «أُمَّكَ، ثُمَّ أُمَّكَ، ثُمَّ أُمَّكَ، ثُمَّ أَبَاكَ، ثُمَّ الْأَقْرَبَ فَالْأَقْرَبَ».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 5139]
المزيــد ...
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce:
Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 5139]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mafi cancantar mutane da yi wa biyayya, da kyautata masa, da kyakkyawar mu'amala, da tsaftatacciyar mu'amala, da abokantakarsa da sadar da zumuncinsa: Ita ce uwa, kuma ya ƙarfafa haƙƙin uwa akan waninta da maimaitawarsa sau uku; dan bayanin falalarta akan ragowar mutane ba tare da togancewa ba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai bayyana wanda yake biye mata a biyayya: Sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci daga 'yan dangi, kuma a duk lokacin da ya zama ya fi kusanci to ya zama mafi cancanta da sadar da zumunci daga mafi nesa.