عن علي رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«رُفِعَ الْقَلَمُ عن ثلاثة: عن النائم حتى يَسْتَيْقِظَ، وعن الصبي حتى يَحْتَلِمَ، وعن المجنون حتى يَعْقِلَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 4403]
المزيــد ...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 4403]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin Dora hukunci na (shari'a) wanda yake lazimtar 'ya'yan Adam ne sai waɗannan ukun:
Ƙaramin yaro har sai ya girma ya balaga.
Da mahaukaci wato mara hankali har sai hankalinsa ya dawo gare shi .
Da mai bacci har sai ya farka.
Ɗora shari'a haƙiƙa an ɗauke musu ita, kuma aikata laifinsu ba'a rubuta musu, sai dai ana rubuta alheri ga yaro ƙarami banda mahaukaci da mai bacci; domin su suna cikin wadanda ibadarsu ba ta inganta ba daga gare shi saboda gushewar ji.