عن عَبْد اللَّهِ بْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قال: «أّعْتَمَ النَبِيُّ -صلَّى الله عليه وسلَّم- بِالعِشَاء، فَخَرَج عُمَر فقال: الصَّلاةَ يا رسول الله، رَقَد النِسَاءُ والصِّبيَان. فَخَرَجَ ورَأسُهُ يَقطُر يقول: لَولاَ أن أَشُقَّ عَلَى أُمَّتِي -أو على النَّاس- لَأَمَرتُهُم بهذه الصَّلاة هذه السَّاعَة».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Annabi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba,siai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci,sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokaci
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya jinkirta fitowa zuwa ga sallar issha'i har dare yayi ,mata da yara sun kwanta bacci,wanda basu da jumurin jira mai tsawo,sai Umar Dan Khaddab ya zo wajensa yace: sallah,mata da yara sun yi bacci. sai Manzo tsira da aminci ya fito daga gidansa zuwa masallaci kansa yana digar da ruwan wanka yana bayyana cewa mafi kyawun liokacin sallar issha'i shine a jinkirta ta.ba don gudun wahalar jiran lokacin ba:ba don kan in matsawa al'umma ta ba da na umarce su da wannan sallar a irin wannan lokacin

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin