عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
كان رسولُ الله صلى الله عليه وسلم إذا عَطَس وضَعَ يَدَه -أو ثوبَهُ- على فيهِ، وخَفَضَ -أو غضَّ- بها صوتَهُ.  
                        
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن أبي داود: 5029]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi. 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] -  - [سنن أبي داود - 5029]                                            
                        (Annabi) tsira da  amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi  atishawa:
Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa.
Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.