عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الجَنَابَةِ، غَسَلَ يَدَيْهِ، وَتَوَضَّأَ وُضُوءَهُ لِلصَّلاَةِ، ثُمَّ اغْتَسَلَ، ثُمَّ يُخَلِّلُ بِيَدِهِ شَعَرَهُ، حَتَّى إِذَا ظَنَّ أَنَّهُ قَدْ أَرْوَى بَشَرَتَهُ، أَفَاضَ عَلَيْهِ المَاءَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ غَسَلَ سَائِرَ جَسَدِهِ، وَقَالَتْ: كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ، نَغْرِفُ مِنْهُ جَمِيعًا.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 272]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka, sannan ya tsettsefe gashinsa da hannunsa har sai ya tabbar cewa ya jika fatarsa, sai ya zuba ruwa akansa sau uku, sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Ta ce: Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya daya muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 272]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin wankan janaba sai ya fara wanke hannayensa, sannna ya yi alwala kamar yadda yake alwalar sallah, sannan ya zuba ruwa a jikinsa, sannan ya tsattsefe gashin kansa da hannayensa, har sai ya tabbar cewa ruwa yakai tushen gashin, ya jika fatar, sai ya zuba ruwa akansa sau uku sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kwarya daya, muna kanfatowa daga gareta gaba daya.